Alwashin da na sha domin inganta aikin saja – Janar Buratai

0

Babban Hafsan Askarawan Najeriya Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa ya zama shugaban sojojin ne tare da shan alwashin inganta tsarin aikin soja domin jami’an sojojin Najeriya su zama kwararru a kowane fanni na ayyukan su.

Buratai ya yi wannan jawabi ne a wurin taron Kungiyar Editocin Najeriya na 13, wanda ke gudana a Fatakwal, Babban Birnin Jihar Ribas.

Ya ce ya yi matukar kokari wajen kara cusa wa sojoji da’a, biyayya, kishin kasa da kuma kishin aikin da su ke yi.

Haka kuma ya ce daga lokacin da ya kama ragamar jagorancin sojojin, ya kara musu karsashi da kwarin guiwar tunkarar Boko Haram.

Ya na mai cewa a lokacin da ya hau jagorancin, Boko Haram sun yi wa kasar nan mummunar illa, ba kan fararen hula kadai ba, abin ya shafi har da su kan su sojoji.

Daga nan sai ya kara tuna wa masu saurare cewa kafin ya hau, Boko Haram sun kashe jama’a da dama, kuma abin bakin ciki an rasa sojoji da dama.

Buratai ya ce kwazo da kishin da ya kara saka wa sojoji a zukatan su ne ya kawo ga nasar da aka samu zuwa yanzu.

Tare kuma da cewa irin atisaye da rawar-daji da horon da jami’an sojoji ke yi, duk ya na daga cikin alwashin da ya dauka na samar da kwararru, nagartattu da kuma zaratan sojoji da za a ci gaba da alfahari da su.

Kwamandan Bataliya ta shida, Manjor Janar Udoh ne ya wakilci Buratai a wurin taron.

Share.

game da Author