Cikin watanni 8 jihar Kaduna ta karbi harajin sama da biliyan 15

1

Shugaban hukumar karba da tara kudaden haraji na jihar Kaduna KDIRS Mukhtar Ahmed ya ce jihar Kaduna ta karbi kudaden haraji a jihar da ya fi biliyan 15 daga Janairu zuwa Agustan 2017.

Mukhtar ya fadi haka ne da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai a Kaduna.

Yace duk da cewa basu samu yadda suke so ba na samo akalla biliyan 50 a wannan shekara , zasu ci gaba da kokarin ganin an wuce abin da aka samu yanzu.

Jihar Kaduna dai itace jiha ta farko da ta fara yin asusun gwamnati na bai daya wato TSA.

Share.

game da Author