Hukumar Hisba a jihar Kano ta kawar da mabarata 1,429 daga titunan jihar a cikin watani takwas (daga watan Janeru zuwa Agusta).
Jami’in hukumar Dahiru Mohammed ya Sanar da haka da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kano ranar Litini.
Ya bayana cewa 420 daga cikin mabarata 1,429 yara kanana ne sannan 1009 manya ne.
Ya ce sun kama mabaratan a hanyoyin Lodge Road, mahadar hanyar Magwan, Kwari, Katsina Road da Wapa.
Dahiru Mohammed ya kara da cewa 860 daga cikin mabaratan mazauna jihar Kano ne,551 kuwa daga jihohin Jigawa,Kaduna, Katsina da Neja sannan 18 daga kasar jamhuriyar Chadi.
Ya ce hukumar ta sako wadanda suka karya dokar jihar da wadanda suke da tabuwan hankali sannan sun madai sauran zuwa jihohinsu.
Daga karshe Dahiru Muhammed yace hukumar ta kamala shirin koyar da mabaratan sana’o’in hannu domin hana su bara a titunan jihar.