Buhari ya jajanta wa mutanen jihar Benue

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa mutane da gwamnatin jihar Benue sanadiyyar ambaliyar ruwan da aka yi a jihar.

Ya umurci hukumar bada agaji na kasa NEMA da ta gaggauta kai tallafi ga mutanen da ambaliyar ya shafa.

kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rawaito cewa wuraren da ambaliyar ruwan a shafa sun hada da gidan radion jihar, kasuwan Wurukum da kuma gidajen mutane sama da 100,000 a kananan hukumomi 12 dake jihar.

Buhari ya ce gwamnati za ta kirkiro hanyoyi da mutane domin gujewa sake faruwar haka.

Share.

game da Author