Zanga-Zangar da muka yi ne ya sa Buhari zai dawo – Kungiyar Charly Boy

0

Kungiyar nan da ke kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dawo ko ya sauka ta ce zanga-zangar da ta gufdanar ne ya sa shugaban kasa zai dawo kasa yau.

Daya daga cikin jaogorar tafiyar Deji Adeyanju yace zanga-zangar da suka yi tayi ne ya sa Buhari zai dawo kasa Najeriya yau.

“ Zanga Zangar mu tayi amfani domin da ba mu yi haka ba da sai dai ayi ta binshi can Ingila mai makon ya dawo kasa inda ake bukatarsa”

Deji ya ce duk da cewa sun sami matsala a Abuja suna shirin ci gaba da zanga-zangarsu A legas daga mako mai zuwa.

Share.

game da Author