Zan koma PSG – Inji Neymar

0

Shahararren dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona ya sanar da kungiyar cewa yana so ya bar kungiyar zuwa kungiyar kwallon kafa ta PSG dake kasar Faransa.

Ko da yake Neymar na da kullalliyar alkawari tsakanin sa da Barcelona cewa duk wanda zai siye shi sai ya biya kudin da ya kai Euro miliyan 222 kafin a yarda a siyar da shi.

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta ce a shirye take ta biya wadannan kudade da aka sa kan Neymar.

Yanzu dai aski ya zo gaban gashi domin ko a karisa ne ko a barshi haka babu kyan gani.

Bayanai sun nuna cewa mahaifin Neymar ya gama tattaunawar kuma shi kanshi dan kwallon ya nuna cewa yana son ya koma PSG din.

Share.

game da Author