Za a yi wa dan majalisa Abubakar Kuki kiranye

0

Hukumar zabe INEC ta sanar da karbar takardu daga mazabar Bebeji don yi wa dan majalisar su a majalisar Wakilai Abubakar Kuki kiranye.

Darektan yada labarai da wayar da kan jama’a na hukumar Adedeji Soyebi ya ce tuni hukumar ta sanar wa dan majalisan abin da ke faruwa don ya kwana da shiri.

Ya kuma ce nan bada dadewa ba hukumar za ta fito da jadawalin ranakun da za a fara maganan yi masa kiranyen.

Hukumar INEC ta ce wannan shine karo na biyu da za a turo mata bukatar haka.

Bayan na Sanata Dino Melaye yanzu kuma ga wannan.

Share.

game da Author