Za a gyara gidan tarihin Sukur da Boko Haram ta Kona a jihar Adamawa

0

Hukumar kula da gidajen tarihi ta kasa NCMM ta ce za ta gyara gidan tarihin Sukur wanda Boko Haram ta kona a shekaran 2014 a dake jihar Adamawa.

Shugaban hukumar NCMM Yusuf Usman ya sanar da haka a lokacin da yake hira da kamfani dillancin labaran Najeriya a Abuja ranar Litini.

Yusuf Usman ya kara da cewa gyaran da za su yi zai hada da na jihar Osun dake Osogbo.

Ya kuma mika godiyarsa ga hukumar UNESCO da ta yi alkawarin tallafa wa gwamantin Najeriya da gyare- gyaren gidajen tarihin kasar.

Yusuf Usman ya ce babbar matsalar da kasar ke fama da shi shine rashin tattalin gidaje da wuraren da ke da tarihin wanda dalilin haka ake rasa masu yawan bude ido ziyartar Najeriya domin ganin irin wadannan wurare.

Tarihi ya nuna cewa masarautan Dur ta samar wa kasa Najeriya da ma’adanar karfe daga karni na farko zuwa karni na 20.

Wurin tarihi na ‘Sukur’ na karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa a kan tsaunikan Mandara dake kusa da bodar Kamaru.

Share.

game da Author