Kamfanin da ke kula da kaddarorin Arewa NNDC ta na tattaunawa da wata kamfanin kasar Turkiyya don sake farfado da masakar KTL.
Shugaban kamfanin NNDC Ahmed Musa ya ce za a saka Dala miliyan 15 don farfado da kamfanin tare da hadin guiwar wannan kamfanin na kasar Turkiyya da gwamnatin tarayya.
Kamfanin kasar Turkiyya zata samar da kashi 35 na kudaden da za a saka, gwamnatin tarayya zata samar da kashi 45 sannan ita kuma kamfanin KTL din ta sa kashi 20.
Kamfanin ta ce sun tafi ran gadin kamfanin tare da tawagar kamfanin kasar Turkiyya din.
Bayan haka NNDC ta ce idan aka farfado da kamfanin za ta saka yadukan ma’aikatan tsaro na Soji, yan sanda da sauransu.
Discussion about this post