Yara da ake tilastawa yin kunar bakin waki ya karu a shekaran nan – UNICEF

0

Asusun bada agaji ga kanana yara na majalisar dinkin duniya ta rahoto cewa adadin yawan yaran da Boko Haram ke amfani da su a matsayin ‘yan kunar bakin wake ya karu a shekarar bana.

Rohoton ya nuna cewa mafi yawan yaran da ake amfani da su mata ne ‘yan shekar 15.

“Yara 83 ne Boko Haram tayi amfani da su a matsayin ‘yan kunar bakin wake wanda 55 daga cikin su mata ne sannan 27 maza.”

“Kowa na tsoran kusantan yara kanana wanda hakan ya jefa su cikin mawuyacin hali.”

Bayan haka UNICEF ta amince ta dauki nauyin kula da yaran har na wani tsawon lokaci sannan yayin da ta ke yin hakan za ta tattauna da wasu iyaye don samarwa yaran sabbin iyayen da za su ci gaba da kula da su.

Share.

game da Author