‘Yan sanda sun dakile wani hari da ‘yan fashi suka kai wurin cire Kudi ATM a Kano

0

‘Yan sandan a jihar Kano sun yi arangama da wasu ‘yan fashi a wani wurin cire kudi na ATM dake bakin Otel din ‘Tower Hotel’ a hanyar filin jiragen sama dake Kano.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Musa Majiya ya tabbatar da haka da ya ke amsa tambayoyi daga wakilin PREMIUM TIMES ta wayar tarho.

Bayan haka ya kara da cewa ‘yan fashin sun so su kwace kudaden mutane ne bayan sun ciro daga wannan na’uran da misalin karfe biyu na rana amma hakan bai kai ga faruwa.

Ya ce duk da cewa barin wutan da suka yi ya kai tsawon awowi amma ‘yan sandan sun sami kama barayin biyu.

Musa Majiya ya ce sun kai wani mutum daya asibiti domin raunin harsashin da ya samu a lokacin da ‘yan sanda da ‘yan fashin ke barin wutan sannan za a kai ‘yan fashi biyu da aka kama kotu bayan an gama yin bincike akan su.

Share.

game da Author