‘Yan Bindiga sun kai hari ofishin EFCC a Abuja

0

Wasu yan bindiga sun kai hari ofishin Hukumar EFCC dake rukunin gidaje na Zone 7, Abuja.

Maharan sun kai farmaki ofishin ne da safiyar Laraba inda suka yi ta barin wuta. Koda yake basu sami yadda suke so ba domin jami’an tsaron da ke gadin ofishin suma sun bude musu wuta.

Duk da cewa sun gudu ganin cewa baza su sami yadda suke so ba sun jefar da wata wasika ga shugaban wannan sashe na hukumar mai suna Ishaku Sharu.

Ishaku Sharu ne ke shugabantar sashen da ke kula da bunciken manyan jami’an gwamnati da Sojojin da suka yi ritaya da harkokin da ya shafi musanyar kudaden kasar waje.

Da aka karanta wasikar, sako ce ga Ishaku Sharu na ya kwana da shiri domin suna fakon ran sa.

Share.

game da Author