Yadda mu ka hana majalisa kafa kwamitin bincikar rashin lafiyar Buhari –Hon. Baba

0

Wani Dan Majalisar Tarayya, Hon. Ibrahim Baba, ya bayyana yadda su ka hana yinkurin da wasu mambobi su ka yi na neman a Kafa kwamitin da zai binciki rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari.

Buhari, wanda ya shafe kwanaki 101 a kasar Ingila, a can baya ma ya taba shafe kwanaki 57 a can ya na jinya.

Shugabannin Majalisar dai sun samu matsin-lamba daga ciki da wajen majalisar cewa su kafa kwamitin da zai binciki rashin lafiyar Buhari, ta yadda kwamitin zai yi duba da Sashe na 144 na Kundin Tsarin Mulki, wanda ya bayyana cewa:

“Kashi biyu bisa uku na mambobin majalisa za su iya tabbatar da shugaba ko mataimakin sa ba za su iya gudanar da shugabanci ba, idan…

Aka tabbatar da gamsassun hujjojin rashin lafiya ta hanyar kafa kwamitin auna rashin lafiya da kuma kwamitin duba lafiya a karkashin karamin sashin doka na 4, wanda zai mika wa shugaban majalisar dattawa da na wakilai.

Manufar ta su ta a kafa kwamitin ita ce a samu wasu hujjoji da za su nemi Buahri ya sauka daga mulki.

Sai dai kuma shi Hon. Baba, wanda mamba ne daga Karamar Hukumar Katagum, kuma daga jam’iyyar APC, ya ce ba su yarda yunkurin ya samu karbuwa ba, inda ya ce tunda Shugaban Kasa ya rigaya ya damka mulki ga mataimakin sa, kuma ya ruguto wa Majalisar Tarayya sanarwa cewa zai tafi jiyya, ai magana ta kare babu sauran wani gutsiri-tsoma.

Ya na mai nuni da cewa dama haka dokar kasa ta ce kowane shugaban kasa ya yi, don haka Buhari ya bi doka, babu bukatar a yi masa wani bi-ta-da-kullin kafa kwamiti.

“Ba tun yau su ka fara kitsa wannan kutunguila da algungumancin ba, an kai wata biyu ana kulle-kulle, amma mu ka tsaya kai da fata mu ka ce ba mu yarda ba, domin Shugaba Buhari bai kauce wa dokar kasar nan ba.” Inji Baba.

Share.

game da Author