Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bin umarnin likitoci ne ya sa har yanzu bai dawo kasa Najeriya ba.
Buhari ya fadi haka ne da yake amsa bakuncin wasu masu jami’an gwamnatinsa da suka kai masa ziyara kasar Britaniya.
” Har yanzu ina bin umarnin likitoci na ne domin sune ke da ikon amince min indawo gida ko kar indawo tukuna. Idan da daa ne zan nuna iko don su yarda mini in komo gida amma yanzu na bar komai a hannunsu tukuna zuwa lokacin da suka ga ya dace a sallame ni in dawo gida.”
Buhari ya gode wa mutanen Najeriya da addu’oi da suke ta yi masa na neman samun lafiya.
” Ina matukar mika godiya ta ga ‘yan Najeriya kan addu’oi da suka yi ta yi min. Bayan haka kuma ina jinjina wa gidaje da tashoshin yada labaran Najeriya da suke sanar da ni abubuwan da ke faruwa a kasar ta hanyar labaran da suke yadawa.
Discussion about this post