Wakar rama zagi kan Igbo ta tada kura, Atiku ya ce a hukunta mawakin

3

Wata waka da aka watsa a soshiyal midiya wadda za a iya cewa zambo da zagi ce ga kabilar Igbo, ta tada kura a kasar nan, tun bayan da wata kafar yada labarai ta Turanci ta watsa ta, bayan ta fassara baitocin ta da Turanci.

Wakar wadda aka yi da Hausa, kamar raddi ce ga irin cin fuska, zagi da aibatawar da magoya bayan kafa kasar Biafra, hususan kabilar Igbo ke wa Hausawa da Fulani, su na kiran su da sunayen dabbobin gida da kuma nau’i’in namun daji daban-daban.

Sai dai kuma alamomi da dama na nuni da cewa hankalin jama’a, musamman ‘yan kudu ya tashi bayan bullar wannan waka, wadda su ke kallon wata barazana ce ga zaman lafiyar kasar nan.

Tuni Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya fitar da sanarwar yin tir da wakar, tare da yin kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kamowa tare da yin hukunci mai tsanani ga wanda ya yi wakar.

Atiku ya yi gargadin cewa da irin haka rikici ya fara barkewa a kasar Riwanda, bayan wani mawaki ya yi wakar nuna tsanar kabilar Hutu.

Sai dai kuma wasu da dama na masu ra’ayin cewa su fa ba su ga aibin wakar ba, domin a cewar su, rama zagi ne da kabilar Igbo ke yi wa Hausawa da Fulani, tun bayan faduwar zaben Goodluck Jonagthan, bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya h au mulki.

Wani bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar, ya tabbatar da cewa tun bayan da Nnamdi Kanu ya fara kada gangar tawaye, ya rika zagin ‘yan Arewa, musamman Hausa Fulani, inda ya ke kiran su da sunan dabbobi daban-daban.

Shi kan sa Nnamdi Kanu, shi ne a sahun gaba wajen zagi da aibata ‘yan Arewa a cikin haramtaccen gidan radiyon da su ka kafa da kuma wurin taruka daban-daban.

Har ila yau, a shafukan soshiyal midiya irin su Facebook, Twitter, Instagram da Whatsapp, a kullum ana ganin rubuce rubuce na batunci da zagi wanda ‘yan asalin Kudu-maso-Arewacin kasar nan ke yi kan Hausawa da Fulani.

Alamomi da dama da kuma kalaman da ke fitowa daga bakin dimbin jama’a a Arewa, bas u jin dadin wannan zagi da muzantawar da ake yi musu.

Idan ba a manta ba, a kokarin sa na nuna goyon bayan Nnamdi Kanu, dan taratsin kushe ‘yan Arewa, Femi-Fani Kayode ya ragargaji Shehu Danfodiyo a shafin sa na Facebook, a farkon watan Yuli, inda ya kira shi da sunaye na aibatawa da muzantawa.

Wata majiya ta bayyana bacin rai ganin yadda duk zagin da kabilar Igbo ke wa Hausawa da Fulani, bai jan hankalin manyan kasar nan ko mahukunta su tsawatar musu, amma duk abin da wasu ‘yan Arewa za su ce kadan kyes, sai a yi ta yayata shi a kakafen yada labarai.
“Wani matashi mai suna Jabir, ya bayyana cewa; “Dan kabilar Igbo wanda ya iya rubutu ya kira ni ‘bastard’, to ni kuma idan waka na iya, ban iya rubutu ba, sai na yi waka na kira shi ‘shege’, ai an yi kunnen-doki ko canjaras kenan.”

Tuni dai wadansu da abin ya dame su su ka fara tunanin cewa ya kamata a shawo kan kallon-hadarin-kajin da matasan kabilar Igbo magoya baya da mabiyan dan tawaye Nnamdi Kanu da kuma matasan Arewa ke yi.

Share.

game da Author