Tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Garba Muhammad Gadi ya rasu ne yau a wani asibiti da ke kasar India.
Garba Gadi ya rasu ya bar mata 3 ya’ya 15.
Garba Gadi shi ne tsohon mataimakin Isa Yuguda kafin su sami rashin jituwa da yaki bin gwamnan lokacin da ya canza sheka daga jam’iyyar ANPP zuwa PDP.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ta hannun kakakinsa Garba Shehu, ya na cewa Garba Gadi mutum ne mai dattaku da sanin ya kamata.
Ya yi adduar Allah yayi masa rahama.
Discussion about this post