Tsohon gwamnan jihar Taraba na rikon kwarya Garba Umar ya canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Garba Umar yace ya yanke shawaran canza sheka ne ganin cewa APC ne zai iya hada kai da mutanen dake da irin ra’ayinsa domin samar da ci gaba a jihar.
Ya ce idan suka mai da hankali sannan suka hada kai wuri daya to za su iya kwato mulkin jihar daga hannun jam’iyyar PDP mai ci yanzu.