A cikin wannan tatttaunawa ta musamman da Ashafa Murnai na PREMIUM TIMES, Shugaban Kungiyar ’Yan Gwangwan na Kasuwar Tipper Garage da ke Gwarimpa, Ibrahim Bagobiri, ya bayyana yadda ‘yan sandan da ke gadin gidan Jonathan su ka matsa masa lamba har ya je gidan, su ka fara sayar masa da wasu suturu daga cikin kayan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan.
PTH: Mu fara da gabatar mana da kan ka.
IBRAHIM: Suna na Ibrahim, amma an san ni a matsayin Shugaban Kungiyar ‘Yan Gwangwan na Kasuwar Tipper Garage, cikin Gwarimpa, Abuja.
PTH: Ko ka san Sajan Musa?
IBRAHIM: Na san Sajan Musa kwarai da gaske, kuma shi ma ya san ni, sama da shekara 12. Ni dai a sanin da na yi masa a baya, na san mutumin kirki ne, wanda ke yawan shigowa kasuwar mu.
PTH:Ta ya aka yi huldar kasuwanci ta shiga tsakanin ka da shi?
Yauwa, bari ka ji yadda aka yi.
Wata rana ne dai a cikin 2016, ina jin tun ma kafin watan azumi ya tsaya, sai ga wani dan aike ya zo wuri na a kasuwa, ya na dauke da suturu guda shida, ya ce min Musa ne ya aiko shi, ya na so na saya. To ni kuma sai mamaki ya kama ni, saboda tun da na ke da Sajan Musa ba mu taba yin wata huldar cinikayya da shi ba.
Nan take sai na kira shi a waya na tambaye shi idan da gaske shi ne ya aiko yaron. Ganin yadda na kafe cewa ni ba zan sayi kayan ba, kuma ina ta yi masa tambayoyi, sai ya fusata, ya ce wato ina zargin sato kayan ya yi kenan?
A nan dai ya mika wa wani jami’in dan sanda waya, shi kuma ya gabatar da kan sa a matsayin Sufeto. Su ka kafe kan cewa lallai wadannan kaya Ogan da su ke aiki a gidan sa ne ya ba su, wato tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan. Kuma su ka ce na zo har cikin gidan Jonathan din domin na tabbatar.
Ko da na je din ma duk na same su a gidan, amma jiki na bai gamsar da ni cewa na sayi kayan ba. Bayan kwana biyu, su ka kara kira na, su na kara tabbatar min cewa shin a matsayin su na ‘yan sanda ya za a yi su saci kaya, kuma a gidan Jonatahan?
Daga nan dai na koma na sayi wadancan set shida. Bayan nan kuma ya sake kira na har gidan na sayi wasu set ‘yan kadan.
To amma a karo na uku da su ka kira ni, sai su ka kai ni su ka bude min wani daki, wanda na ga makare yak e da kaya masu yawan gaske. Su ka ce min duk Jonathan ne ya raba musu, bayan an fadi zabe. Wai sai su ka tara a nan, amma yanzu su na so su sayar.
PTH: To ka sayi tulin kayan da su ka nuna maka din?
IBRAHIM: Ban saya ba. Dama ina shiga dakin sai na yi arba da wani faskeken hoton Jonathan a bango. Nan take na ji gaba na ya fadi, tsoro ya kama ni. Sai na buga salati, har Sajen Musa ya ce min ‘me ka ke wa salati?’ Na ce masa ai cewa na yi ‘Daga Allah mu ka fito, kuma a wurin sa za mu koma.’
Ai a rude na kalli su Sajen Musa na ce:
“Musa, idan na sayi kayan nan, ko da zan fi kowa arziki a Nijeriya, ni ba zan sayaba.’ Saboda kai da ganin kayan ka san ba irin kayan da haka kawai za a dauka a bai wa ‘yan sandan da ke gadin gidan kyauta ba ne.
Ni dai daga nan kusanci na da Sajan Musa ya ja baya, shi kuma sai ya fara neman wasu da zai rika sayar wa kaya.
PTH: Amma kuma akwai tabbacin an fara sayar da wasu kayan a nan kasuwar ku ko?
IBRAHIM: Gaskiya ka fada. Lokacin da na ce wa su Musa ba zan sake sayen kayan ba, sai ya kewaye, ya samu wani ya fara sayar masa. Amma ko da na gano cewa ana sayen wasu kaya a hannun Musa, sai na gardadi kowa na ce daga yau ko tsinken sakace Musa ya kawo, ko ya kira wani ya ce ya je ya saya, to kada wanda ya kuskura ya sake saye daga hannun sa.
Tun daga ranar da na yi wannan gargadin, to a kasuwar mu dai ba wanda ya kara zuwa ya sayi komai a hannun su Sajen Musa. Ka ga ba mamaki sun zagaye wasu kasuwannin gwamgwan kenan sun sayar da kayan, domin akwai hujjojin da su ka tabbatar da haka.
PTH: Me ya sa ba ka dauki wani mataki ba bayan ka fara sayen kayan ka daina?
IBRAHIM: Ai ba ka san ni b a, shi ya s aka yi min wannan tambayar. Bari ka ji, idan wani abu ya hada ka da ‘yan sanda har su ka fara jin haushin ka, musamman a harka irin wannan da ta shafi kayan sata, to tilas ka yi taka-tsantsan, kuma ka iya takun ka. Sannan kuma ka yi kaffa-kaffa da su.
Amma bari na fada maka wani abu, ni mutum ne mai kima da kyautatawa ko kwatanta gaskiya bakin gwargwado. Kai duk wani D.P.O da aka yi a Gwarimpa a cikin shekaru 12 din nan, ba wanda bai san ni ba. Haka su ma ‘yan sandan Gwarimpa duk sun san irin kokarin da mu ke yi wajen taya su kama barayin da su ka saci kaya, su ke kokarin saidawa a kasuwa.
Mu dama daga cikin dokokin kungiyar mu da shaduddan sana’ar mu, kada mutum ya kuskura ya sayi kayan sata. Kungiyar mu na da kwamiti wanda ke tantance mai sayarwa da kuma kayan da za a sayar din.
Matsawar mu ka fara zargin kayan na sata ne, to sai mu gaggauta damka kayan da wanda ya kawo mana kayan ga ofishin DPO na Gwarimpa. Mun sha yin haka, kuma ni da kai na ke zuwa na rubuta sitatimen cewa na damka kaya kaza da kuma wane kaza da ake zargi, ko aka kama da kayan sata.
PTH: To Ibrahim me ya sa ka gudu ka buya?
IBRAHIM: Wallahi ni fa ba tsoro ne ya sa na gudu ba, na janye jiki na daina zuwa kasuwar ne, saboda kunyar alakanta mu da sayen kayan sata da aka yi, alhali ni ban sani ba. Don ni ‘yan wadanda na saya din ma ce min su ka yi Ogan su ne ya ba su kyauta.
Kowa ya san mu na da doka ta kin sayen kayan sata. Su ma jami’an ‘yan sandan Gwarimpa sun sani, sun kuma san irin taimakon da mu ke yi masu wajen kama kayan sata. Za ka iya zuwa dibijin na ‘yan sandan Gwarimpa ka tabbatar da haka.
Ni daga yanzu na dauki darasi, na daina saurin amince wa mutum haka kawai, sai na yi masa sani na hakika, ba sanin-shanu ba.