TAMBAYA: Menene ainihin bayanin wannan ayar “ Azzani la yankihu illa Zaniyatan Aw Mushrikatan…”
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
FASSARAR AYA TA UKU A CIKIN SURATUN NUR WATO SURA TA 24 AYA TA 3
“الزَّانِي لَا يَنْكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً
وَالزَّانِيَةُ لَا يَنْكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ وَحُرِّمَ
ذَلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ” (سورة النور آية ۳)
inda Allah ya ke cewa “Adhdhani la yankihu illa dhaniyatan Aw Mushrikatan wadha-dhaniyatu la yankihuha illa dhanin aw mushrikun, wa hurrima dhalika alal mu’munin” (Q24:3)
GUNDARIN FASARAR WANNAN AYA IT ACE
“ MAZINACI BAYA AURE FACE DA MAZINACIYA KO MUSHIRIKA, KUMA MAZINACIYA BABU MAI AURENTA FACE MAZINACI KO MUSHIRIKI .
KUMA AN HARAMTA WANNAN A KAN MUMINAI”
Ma’anar Ayan kuma shi ne: Mazinaci baya saduwa ko jima’i da kowa face da mazinaciya lalatacciya kamarsa ko kuma mushirika wanda bata dauki zina haramun ne ba, sannan kuma mazinaciya babu mai aikata alfasha (zina) da ita face mazinaci, fasiki lalatacce kamarta ko mushiriki mare addini. Kuma Allah ya
haramta zina ga muminai.
Kalmar AURE da aka ambata a wannan aya tana nufin SADUWA ko JIMA’I ta hanyar zina. Kalmar bata nufin aure.
Domin NIKAH a larabci shi ne WADA’U wato, jima’i ko saduwa. A musulunce, sai larabawa suke kiran NIKAH aure domin aure shi ne ke hallata saduwa tsakanin miji da mata.
Manyan malaman Tafsiri kamar Ibn Abbas, Mujahid, Ikrimah, Sa’idu Bn Jubair, Urwah, Dahhak, Makhul da Muqatil haka suka fasara wannan aya.
Idan aka fassara ayar da ma’anar aure, akwai cin karo a ciki a mu’amalar al’uma. Akan samu mazinaci ya aure salihar mata da bataba yin zina ba.
Kuma akan samu mazinaciya ta aure miji salihin bawa bai taba yin zina ba. Gashi ayar kuma tana cewa “Mazinaci baya aure face da mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya babu mai aurenta face
mazinaci ko mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan muminai”
To idan aka baiwa ayar wannan ma’ana na aure, to yaya za’a yi da salihar matar da ta aure fasiqi ko salihin mijin da ya aure fasika?
Don haka Ibn Abbas da sauran malaman Tafsiri da na larabci suka tabbatar da cewa ayar na nufin cewa Fasiqi baya zinar sa sai da fasika ‘yar uwarsa ko mushirika mare addini,kamar yadda itama fasika bata alfasha sai da mazinaci dan-uwanta ko mushiriki. Kuma muminai basa
zina don Allah ya haramta musu ita.
Allah ya tsaremana imaninmu da mutuncinmu. Amin