Cibiyar da ke samarwa da adana jini ta kasa NBTS ta yi kira ga mutanen da su yawaita zuwa cibiyar don ba da gudunmawar jininsu. Yin hakan zai taimakawa mabukata da marasa lafiya.
Jami’in hukumar NBTS Nnamdi Agu ya sanar cewa wannan sanarwa da yake yi ya zama tilas ganin cewa cibiyar na fama da karancin jinni sannan mabukata na nan na ta nema.
Ya ce babbar dalilin da ke hana mutane bada jinin su shine rashin sanin amfanin da jininsu kan iya yi wa marasa lafiya idan har suka ba da shi sannan da tsoron da suke dashi cewa kila suma za su iya fadawa cikin wani irin rashin lafiya don haka.
Ya roki mutane da su dinga taimakawa marasa lafiya kan haka.