A yau Talata Shugabannin rundunoni sojin Najeriya da ya hada da na Kasa, Ruwa da na sama suka amsa umarnin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo kan su koma Maiduguri domin magance hare –haren da Boko Haram ke yi a jihar Borno.
A makon da ya gabata ne Osinbanjo ya umurci su da su koma Maiduguri bayan ya tattaunawa da su akan yadda za a magance aiyukkan Boko Harm a yankin arewa maso gabacin kasarnan.
Bayan kisan ma’aikatan hako danyen mai a yankin Chadi tare da wasu jami’an tsaron da ke tsare da su da wasu malaman jami’ar Maiduguri wanda biyar daga cikin su suka rasa rayukan su a cikin makon da ya gabata,Boko Haram ta kai hare –haren da ya kai sau 90 a cikin gari da bayan garin Maiduguri a cikin watani hudu.
Shugaban sojin sun isa garin Maiduguri damisalin karfe 11 na safiyar yau.