Bayan ikirari da cika-baki da sojoji su ka sha yi cewa sun kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yanzu kuma rundunar sojojin ta bayar da umarni ga jami’an ta su kamo Shekau a duk inda ya ke a cikin kwanaki 40 kacal.
A cikin wani sa jawabi da kakain askarawan Najeriya, Sani Usmana ya sa wa hannu, Babban Hafsan Hafsoshin Kasar nan, Tukur Buratai, ya bayar da wannan oda ne ga kwamandan zaratan sojoji ‘yan ina-damutuwa, Operation Lafiya Dole, Ibrahim Attahiru.
Shekau, wanda dan asalin jihar Yobe ne, ya hau shugabancin Boko Haram tun bayan kashe shugaban kungiyar na farko, Mohammed Yusuf a cikin 2009. Sojoji sun sha bayyana cewa sun kashe shi.
Sai dai kuma sojojin Shekau din ainihi tuni ya mutu, wanda ke ikirarin shi ne Shekau a yanzu, na bogi ne kawai.
Su kuma ‘yan kungiyar sun sha cewa shugaban su Shekau na nan daram da ran sa.
A duk lokacin da aka bayar da sanarwar cewa an kashe Shekau, sai ya bayyana ya ce ga shi da ran sa, ba a kashe shi ba. Amma akwai wasu da ke nunu da cewa ba ainihin Shekau din ba ne ke fitowa ya na magana, wani ne daban.
LOKUTAN DA AKA RKA YIN IKIRANRIN KISAN SHEKAU
2009: Jami’an tsaron kasar nan sun ce sun kashe Shekau tare da shugaban kungiyar, Mohammed Yusuf, da kuma sauran ‘yan kungiya alalla dubu daya.
Yuli 2010: Shekau ya fito a cikin bidiyo ya na ikirarin kasancewa sabon shugaban Boko Haram.
2011: Sojoji sun ce akwai alamun da ke nuna cewa an kashe Shekau yayin wata musayar wuta da jamai’an sojoji.
Afrilu 2011: Shekau ya fito a cikin bidiyo ya na cewa makaryata ke yada labarin mutumwar sa.
Shekau wanda ya yi magana da Hausa, cewa ya yi “Haka a koda yaushe makaryata ke shiga radiyo sun a kitsa karyar cewa sun kashe ni.
Ya ce “to yau za ku kure ramin karya. An ce an kashe ni, amma ku kalle ni, ga ni da lafiya ta garau.
Daga nan kuma sai kakakin sojojin na lokacin, Sagir Musa ya ce rahotannin sirri sun tafi a kan cewa an kashe Shekau a rananr 30 Ga Yuni, 2013 a Dajin Sambisa.
Satumba 2013: An nuno bidiyo ida Sheaku ya ce “A sani ba zan mutum ba, sai Allah ya karbi ran na.”
24 Ga Satumba, 2014: Sojoji sun ce sun kashe Shekau a wani artabau da ka yi da shi a Yakin Konduga, wanda aka fafata a ranakun 12 da 14 Ga Satumba.
Wannan ikirari da sojojin Najeriya su ka yi, su ma na Kamaru sun jaddada faruwar hakan.
Sojojin Nijeriya su ka ce tun shera daya baya su ka kashe Shekau, kawai dai wani Shekau din Bogi ne ke karyar cewa shi ne Shekau.
‘’Sabon Shekau ne aka kashe a Konduga, kusa da Maiduguri.”
Olukolade ya ce sabon Shekau din sunan sa na ainihi Mohammed Bashir, amma kuma ya na da inkiya da dama, kamar Abubakar Shekau, Abacha Abdullahi Geidam da Damasack.