Sarkin Lere Abubakar II ya ziyarci El-Rufai

0

Mai martaba sarki Lere Janar Abubakar Mohammed II (rtd) ya yi wa gwamnan jihar Kaduna ziyarar gaisuwa da mika godiyarsa ga ayyukan ci gaba da ya kawo garin Lere da yankin masarautarsa.

A watan da ya ga bata ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da kafa wani sashe na jami’ar jihar a garin Lere.

Gwamna El-Rufai da wasu jami’an gwamnatin jihar da suka hada da kwamishinan ruwa na jihar Suleiman Aliyu Lere, Kwamishinan Kasafin kudi da shirye-shirye Mohammed Sani Wamban Lere Alhaji Bashar Umaru, shugaban (RUWASSA) ne suka tarbi Sarki Abubakar a fadar gwamnatin jihar.

A tawagar sarki, akwai Magajin Garin Lere, Iyan Lere, Sa’in Lere, Sarkin Sudan na Lere, Majikiran Lere, da wasu hakimai da masu sarauta na garin Lere.

Share.

game da Author