Sanata Shehu Sani ya tallafawa sansanin yan bautar kasa a Kaduna da magunguna

0

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ba da kyautar magunguna ga sansanin masata masu bautar kasa dake jihar Kaduna.

Sanata Sani wanda wani maitaimaka masa Abdussamad Chima Amadi ya wakilta ya ce yayi haka ne domin tallafa wa matasan da suka zo jihar domin gudanar da aikin bautar kasa.

Da ya ke karbar magungunar a madadin daliban shugabar hukumar NYSC na Kaduna Bello Ballama da darektan sansanin Haiba Salisu sun gode wa Sanatan kan wannan hidima da yayi wa matasan da suke zo aikin bautar kasa jiha. Sun kara da cewa za suyi amfani da wadannan magunguna yadda ya kamata.

Share.

game da Author