Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kammala shirin fara horas da dakarun tsaro na ‘Civili defence’ da na ‘yan sandar kasar nan.
Rundunar sojin ta ce za ta yi haka ne don koyar musu da dabarun yaki saboda aikin samar da tsaro da ake yi musamman wanda ya shafi Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.
Ministan tsaro Mansur Dan-Ali ne ya sanar da haka a taron yaye daliban makarantar sojojin Najeriya dake Buni Yadi a jihar Yobe.
Ya kara da cewa an yi shirya haka ne don a a sami Karin kwararrun dakaru da za su taimaka wa sojoji wajen yaki da Boko Haram.
Ministan ya ce za su horar da su a karamar hukumar Bama, dake jihar Barno.
Discussion about this post