Sanatoci masu wakiltan Kaduna ta tsakiya da Sanata mai wakiltan Kaduna ta Arewa Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi ne suka kai kukan su hedikwatar jam’iyyar a Abuja.
Sanatocin sun koka da yadda jam’iyyar a jiha ta kudanar da zaben daliget da akayi a jihar.
Shugaban jam’iyyar ya ce jam’iyyar za ta duba wannan korafi da sukeyi akan zaben domin warware matsalar.
John ya kara da cewa jam’iyyar bata ji dadin abubuwan da ya faru a jihohin Kaduna da Ribas ba.