Ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2017 ne Allah yayi wa Alhaji Aminu Idris Daura rasuwa a jihar Katsina.
Alh. Aminu Idris Daura ya rau ne bayan gajeruwar rashin Lafiya da yayi fama da shi.
Kamar yadda babban dan marigayin ya sanar anyi jan’izar mahaifin nasa ne a garin Katsina.
Dubban mutane ne suka halarci jana’izar inda har yanzu ana karbar gaisuwa a gidan mamacin dake Unguwar Tudun Wada, Katsina.
Wasu mazauna unguwar Tudun Wada da wasu yan asalin jihar Katsina sun nuna jutyayin su akan wannan rashi na Alh. Aminu Idris Daura.
“ Alh. Aminu ubane ga kowa da kowa a wannan unguwar sannan ba unguwar Tudun Wada ba har wasu unguwanni dake cikin garin Katsina sun ji wannan rasuwa. Mutum ne mai nuna kowa nasa ne. Ya taimaka wa matasa da mutane da dama a jihar.” Inji Sani Saiba
Ita ko Hajiya Zuwaira cewa tayi kamar yadda taji rasuwar mahaifinta haka taji rasuwar Alh.Aminu Idris.
“Mu fa uba ne a garemu kuma babu abin da zaka je mishi da shi sai yayi kokarin ganin ya agaza maka. Wanna rashi na jiha ce gaba da ban a yan uwanshi da mu ba.
Wani Jami’in gwamnatin jihar Katsina, Alh. Kabiru Sanusi, ya jinjina wa marigayi Alh. Aminu Idirs, inda ya ce “ Rabon da inji mutuwa irin haka na dade. Alh. Aminu Gogaggen ma’aikacin gwamnati sannan mutum ne mai kamala da dattaku. Jihar Katsina tayi rashi, Ba karamin rashi ba.
Babban dan marigayin Hashiru Aminu ya ya yi fatan Allah ya jikan mahaifin nasu sannan ya ce lallai za su ci gaba da mutunta jama’a kamar yadda mahaifinsu ya tarbiyartar dasu akai.
Hashiru Aminu wanda fitaccen ma’aikaci ne da ya kware a harkar na’ura mai kwakwalwa wato Komfuta sannan dan Najeriya na farko da ya ke da shaidar cin jarabawar Cisco CCDE ya gode wa yan uwa da abokan arziki da suka halarci ta’aziyyar mahaifin nasu.
” Rashin mahaifi babban abu ne, amma dukkan mu wata rana za mu koma ga Allah. Ina fatan Allah yayi musu rahama ya sa Aljanna ta zamo makomansu, mu kuma Allah ya kyautata namu karshen.” Inji Hashir