Ranar 1 Ga Satumba za a yi Sallah, cewar Sarkin Musulmi

0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi shi da Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci, sun bayyana cewa ranar 1 Ga Satumba, 2017 ce za a gudanar da Babbar Sallah a kasar nan.

Dama dai tun da farko Gwamnatin Saudi Arabiya ta bayyana wannan rana a matsayin ranar 10 Ga Zul Hajji, ranar da za a yin layya a dukkan fadin duniya.

Wannan bayani ya fito daga kamfanin yada labarai na NAN, a Sokoto, a ranar Laraba. Inda rahoton ke nuni da cewa hakan ya biyo bayan ganin sabon watan da aka yi a ranar Talata da ta gabata, watau ranar 22 Ga Agusta, 2017.

Daga nan sai Sarkin Musulmi ya yi kira ga dukkan musulmi su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a kasar nan, domin a samu kwanciyar hankali da ci gaban kasa. Ya kuma yi wa daukacin musulmi fatan alheri.

Share.

game da Author