Ranakun Juma’a da Litinin hutun Sallah ne -Gwamnatin Tarayya

0

Gwamantin Tarayya ta amince da ranakun Juma’a, 1 Ga Satumba da kuma Litinin, 4 Ga Satumba, a matsayin ranakun hutun Babbar Sallah.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau ne bayyana haka, a madadin gwamnatin tarayya, inda ya ke taya daukacin Musulmi da ‘yan Najeriya murna. Ya kuma yi addu’ar gudanar da shagulgulan sallah lafiya, tare da samun zaman lafiya da hadin kan kasar nan.

Dambazau ya kuma roki ‘yan Najeriya su hada hannu da gwamnatin Muhammadu Buhari, domin kai ta gacin kudirin ta na tabbatar da samun ingattacciyar Najeriya.

Ya kuma tabbatar samun zaman lafiya tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ya na mai umartar jami’an tsaro su tabbatar da wanzuwar hakan.

Ministan ya yi tir da munanan kalaman kiyayya ya na mai gargadin masu zuguguta kalaman su kuka da kan su.

Share.

game da Author