PDP za ta kau da Buhari a 2019- Goodluck Jonathan

0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ya na da yakinin cewa jam’iyyar PDP za ta lallasa  APC a 2019.

Jonathan ya fadi haka ne a wajen taron jam’iyyar PDP da akayi a Abuja.

” Yanzu mutanen Najeriya sun ga bambancin da ke tsakanin mu da jam’iyyar da ke ci yanzu. Lokacin mu an sami daidaituwa a farashin abinci da kayan masarufi.”

Jonathan ya kara da cewa muddun aka zabi jam’iyyar PDP zasu dawo da tattalin arzikin kasar kamar yadda take ada.

” A zamanin mulkin PDP ne Najeriya ta yi fice da suna musamman wajen bunkasar tattalin arzikin Kasa. Sannan an sami ci gaba masu yawa a fannoni dabam dabam da ya shafi aiyukan ci gaban kasa.”

Ya ce yana da yakinin cewa mutanen Najeriya sun dawo daga rakiyar jam’iyyar APC kuma a zaben 2019 PDP za ta yi nasara sosai.

Share.

game da Author