PDP ta lallasa APC a zaben Gombe

1

Jam’iyyar PDP ta doke APC a zaben cike gurbi da akayi na dan majalisar dokokin jihar Gombe jiya Asabar.

Dan takaran kujeran dan majalisar Dukku na jam’iyyar PDP Sa’idu Malala ne ya lashe zaben da kuri’u sama da 7000 in da A Inuwa ya sami kuri’u 4000 da yan kai.

A watan Yunin da ya gabata ne Allah yayi wa dan Majalisar dokokin jihar da ke wakiltan karamar hukumar Dukku Gambo Kabade rasuwa.

Jam’iyyu 7 ne suka  takara a zaben.

Share.

game da Author

  • Muhsin saidu

    Your CommentPremium Times Hausa. Ina yi maku fatan alkhairi, Ina jin dadin yadda kuke tsarawa da kuma gabatar da Labarai masu in ganci, Allah ya kara basira amin.