Mutane 140 sun kamu da cutar kenda a jihar Taraba

0

Kwamishinan kiwon lafiya Innocent Vakkai ya ce cutar Kenda ta kama mutane 140 a kananan hukumomi 10 dake jihar Taraba.

Ya fadi haka ne a lokacin da yake hira da manema labarai ranar Laraba inda ya kara da cewa mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar yara ne ‘yan kasa da shekara biyar wanda ba su sami alluran rigakafin cutar ba.

Ya ce cutar Kenda cuta ce da ta fi kama mutanen kasashe mau tasowa kamar Najeriya sannan cutar na daya daga cikin cututtukan da ke sanadiyyar rayukan yara kanana musamman a yankin arewacin kasan.

Innocent Vakkai ya ce gwamnati za ta turo kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya domin yin allurar rigakafi a jihar musamman a wuraren da suke fi kamuwa da cutar.

Ya ce ma’aikatan za su raba katin yin allurar rigakafin da yi wa yara ‘yan watanni tara zuwa watanni 59 allurar rigakafin cutar sannan duk wanda ba su da katin an san cewa basu yi allurar rigakafin cutar ba.

Ya kuma yi kira ga iyaye da su kawo yaran su domin yi musu allurar rigakafin cewarsa hakan zai taimaka wajen kawar da cutar a jihar.

Share.

game da Author