MSF ta bude wurare biyu don kula da yara dake fama da yunwa a Maiduguri

0

Kungiyar likitocin aikin jinkai MSF ta bude wurare biyu domin kula da yara dake fama da yunwa a Maiduguri.

Kungiyar MSF ta bude wuraren ne a Dala da Gwange domin shawo kan matsalar yuwar da yara mazauna sansanonin yan gudun hijra a jihar ke fama da shi.

Kungiyar ta ce a cikin watanni biyar yara sama da 240 sun rasa rayukansu a dalilin yunwa musamman yaran mazauna cikin sansanonin dake Bama da Pulka.

Kungiyar ta ce yin hakan zai rage matsalar karancin wuraren kula da yaran da ke fama da yuwa kuma yanzu haka suna kula da ciyar da yara 4,500 sannan a duk mako suna karbar yara 140 masu fama matsalar yunwa.

Share.

game da Author