Rundunar ‘yan sandan jihar Nassarawa sun bayyana cewa su na tsare da wasu mutane biyu da ake zargin suna daga cikin matasan da suka kashe wani soja mai suna Ayuba Ali, ranar Litinin, a garin Akwanga, Jihar Nassarawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Kennedy Idrisu ne ya sanar da haka ga kamafanin dillancin labarai, NAN, a Lafiya, babban birnin jihar.
Idrisu ya kara da cewa, sojan ya hadu da ajalinsa ne yayin da ya ke kan hanyar sa daga Maiduguri a kan babur. An ce ya banki wani mai talla ne a kan titi daidai Angwan Affi cikin Akwanga.
Kakakin ya ce sojan wanda ke sanye da kayan gida ya yi dukkan iya kokarin sa wajen tarairayar mai tallar da ya banke, inda daga bisani hatsaniya ta barke, aka yi ta dukan sa har ya suma.
Sojan dai ya mutu ne a asibiti, yayin da ake shirya yadda za a kamo sauran wadanda ke da hannu wajen kisan na sa.
Wani da abin ya faru a gabansa ya ce a unguwar kowa ya gudu, saboda tsoron abin da zai iya biyo baya.
“A yanzu din nan da na ke magana da ku, an jibge sojoji cike da motoci hudu a inda abin ya faru, kuma duk inda su ka ga matashi, sai kawai su cafke shi.” Inji John Abimiku.