Malaman Jami’o’I sun fara yajin-aiki

0

Malaman Jami’o’in kasar nan mallakar gwamnatin tarayya, sun fara yajin aikin sai-Baba-ta-gani daga ranar Lahadi, 13 Ga Augusta.

Kungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya, ASSU ce ta bayyana haka a ranar Litinin da safe.

Da ya ke jawabi ga taron manema labarai, shugaban kungiyar, Biodun Ogunyemi, ya bayyana dalilan tafiyar su yajin aikin.

“A iyar tsawon kwanakin da za mu shafe mu na yajin aiki, mun haramta koyarwa ga dalibai, ba za mu gudanar da jarabawa ba, ba za mu zauna wani taro ba, ko ma wane iri ne.” Inji shi.

Share.

game da Author