Wani dan Kabilar Igbo kuma mazaunin garin Daura ya ce makiya sun ji kunya tunda dai gashi Buhari na hanyar dawowa kasa Najeriya yau.
Chukwu ya ce tun da Buhari ya bar kasar nan yake ta yi masa Addu’a don Allah ya bashi lafiya.
Ya ce yau yana cike da farinciki jin cewa Buhari zai dawo kasarnan.
Wasu Mazauna garin Daura sun fito titunan garin suna nuna farincikinsu da dawowar Buhari.
Wani Manomi Nura Abubakar y ace sun dade suna shirya addu’o’I na musamman domin Allah y aba shugaban kasa lafiya kuma tunda har Allah ya sa zai dawo su sun cikin murna.