Majalisa za ta sake duba maganar karancin albashi – Bukola Saraki

0

Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya ce majalisar na shirye don yin gyara ga dokar yadda albashin ma’aikatan kasar nan yake.

Ya fadi haka ne da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abuja. Saraki ya kara da cewa majalisar na sane sannan ta na shirin yin gyara ga wannan doka domin samun kari ga mafi karancin albashin ma’aikaci a kasarnan.

Bukola Saraki ya ce majalisar na jiran fadar shugaban kasa ta turo kudirin yin hakanne kafin su dukufa akai.

Daga karshe ya yi magana kan matsalolin da wasu gwamnoni ke fama da su na rashin iya biyan ma’aikata albashi a jihohinsu. Ya kara da cewa ya tabbatar canza dokar albashin ba zai kawo wata matsala ba domin babu gwamnan da ba zai so ya taimaka wa mutanen sa ba.

Share.

game da Author