Ma’aikatan kiwon lafiya ta ce za ta hada hannu da hukumar kula da hadarukka ta kasa FRSC da sauran masu ruwa da tsaki a harkar sufuri na da hanyoyi na kasa domin ganin an rage yawan hadarukkan da ake samu a hanyoyin kasarnan.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya fadi haka ranar Lahadi da ya amsar bakuntan jami’in majalisar dinkin duniya Jean Todt tare da tawagarsa da suka ziyarceshi a Abuja.
Ya ce sun bude asibitoci na musamman domin kula da mutanen da suka yi hadari a hanyoyin mu, sannan sun samar da motocin daukan mutanen zuwa asibiti da basu kula na kwana daya kyautane a asibitocin.
Karamin ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya ce ma’aikatar su sun horar da ma’aikatan kiwon lafiya domin kula da mutanen da suka sami yi a hanyoyin kasar.
Ya ce wanda suka fara kaddamarwa da shi shine na hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin da aka rufe tashar jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja a watan Afirilu.
Jean Todt ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kafa dokar kare rayukan mutane masu bin hanyoyin kasar.