Likitocin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin sun fara yajin aiki

0

Kungiyar likitoci asibitin koyarwa na jami’ar Ilori UITH sun fara yajin aiki har na tsawon kwanaki biyar.

Likitocin sun fara yajin aikin ne ranar Laraba don nuna fushinsu ga yawan rage albashinsu da hukumomin jami’ar keyi da aka fara tun a shekarar 2014.

Shugaban kungiyar likitocin Ige Kolawole ya ce likitocin asibitin UITH ne kadai ake rage wa albashi.

Shugaban asibitin UITH Abdulwaheed Olatinwo ya ce suna rage albashin likitocin ne saboda karin likitocin 150 da suka yi wanda a ganin kungiyar hakan bai dace ba.

Shugaban kungiyar Kolawole ya zargi asibitin da laifin karya dokar daukan likitoci.

Ya kuma yi kira ga asibitin da ta daina rage albashinsu sannan kuma ta daina karban kudaden fansho a boye.

Ya ce idan har hukumomin jami’ar basu daina haka ba, zasu sanar da hukumar EFCC da ICPC.

Share.

game da Author