LAYYA: Farashin manyan raguna ya kai naira 200,000 a Abuja

0

Yayin da ake kusan rashin kudi sakamakon matsin tattalin arzikin da ake fama dashi, ta yadda har ragunan layya su ka yi arha tibis a wasu garuruwa da dama, a Abuja ba haka abin ya ke ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta kewaya wurin saida raguna na tafi-da-gidan ka kusan guda goma, inda ta gane wa idon ta yadda harkar cinikin ragunan ke gudana.

A cikin Gwarimpa akwai wuraren saida raguna biyar inda tun kwanaki biyar kafin sallah aka fara hada-hadar saida raguna a cikin su.

A wata kasuwar tsaye ta masu saida raguna cikin Gwarimpa, wakilin mu ya cika da mamaki yayin da aka gwada masa wasu girda-girdan raguna guda hudu, da aka tabbatar da cewa an sai da kowanen su a kan kudi naira dubu 180,000.

Daya daga cikin manyan dillalan mai suna Imam Nuhu, ya tabbabatr wa PREMIUM TIMES Hausa cewa: “Ka ga ragunan nan hudu, naira dubu 180,000 mu ka sayar da kowane daya. Wani mutum ne ya zo, ya na ganin su, sai ya sa aka warwe masa, a ka yi ciniki har dai aka sallama masa a naira dubi dari da tamanin.”

Da wakilin mu ya tambayi dillalin me ya sa rakunan ke daure a jikin turakun su, bayan kuma sun ce an sayar da su naira dubu 720 su hudu, sai Imam ya ce, “wanda ya sayi ragunan ya biya naira dubu 500, ya ce a ajiye masa ragunan sa, da safe zai zo da mota tare da cikon kudi ya dauki abin sa.”

PREMIUM TIMES ta tambayi daga cikin manyan dillalan daga inda su ke samun raguna masu yawa haka. Sai ya nuna wasu mutane biyu can a gefe, sannan ya ce: “Ka ga wadancan mutanen, su ne su ke kwao mana raguna daga Sakkwato duk shekara. Mu aikin mu kawai daillanci, mu saida musu kayan su.”

Ya ci gaba da cewa a wannan shekarar sun kawo mana raguna 80. Su kan ba mu farashi, idan mun dan kara wani abu kuma, to na mu ne. wanda ba mu kara ba har ciniki ya tsaya a daidai farashin su, to za su ba mu naira dubu daya a cikin kudin ragon.”

Kafin wakilin PREMIUM TIMES ya bar wurin sai da aka nuna masa ragon naira dubu 200,000, har ma da na dubu dari da goma.

A gefen Abuja da kan manyan hanyoyin shiga birnin, duk inda ka duba garuna ne ana ta hada-hada. Sai dai kuma wani bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar, ya tabbatar da cewa hada-hadar ragunan layya a Abuja cike ta ke da matsaloli da kuma harkalla.

Shu’aibu, wani mai jigilar kawo raguna daga Sakkwato, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa: “Hukumar Kula da Tsaftace Abuja, wato Abuja Environmental Protection Agency ta na takura musu matuka.

“A duk shekara kafin mu fara wannan sana’a sai mun biya kudin haraji naira dubu hamsin ga wannan hukuma, sannan za mu fara sauke ragunan mu. Amma duk haka wannan bai hana wasu lokuta su zo su kawo samame, su kwasar mana raguna.

Tilas sai mun bi har can ofishin su, mun karbo ragunan mu bayan mun yi masu ihsani na kudi masu dama.”

Ko ana kwana biyu kafin sallah, PREMIUM TIMES Hausa ta tabbatar da cewa sai da Hukumar Kula da Tsaftace Abuja ta daka wasoson raguna hudiu, a wata masaida raguna, a cikin Gwarimpa. Masaida ragunan na kusa da wani gida mallakar Janar Aliyu Gusau, mai ritaya.

“Amma daga baya mun je mun karbo ragunan mu. Sai dai ka san Hausawa sun ce ba a yin bari a kwashe daidai.” Haka wani dillali ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA.

Wani bincike kuma ya tabbabatar da cewa a sheakrar da ta gabata, Hukumar Kula da Tsaftace Abuja ta rika bi da babbar mota tirela a kan hanyar Kubwa, har sai da ta kwashe raguna sama da 200. Majiyar da abin ya shafa ta shaida wa wakilin mu cewa sai da masu ragunan su ka rika zuwa “har ofishin hukumar, alkalin kotun tafi-da-gidan ka ya yi musu tara su ka biya, sannan aka ba su ragunan su.

Wani Alhaji Umaru, wanda ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa ya je sayen rago ne, ba dillanci ya ka kai shi ba, ya ce shi bai ga dalilin da zai sa a rika takura wa masu hada-hadar ragunan nan ba.

“Gaba daya fa harka ce ta kwanaki uku zuwa hudu. Daga bana fa sai badi. Ina su ke so mu rika zuwa mu na sayen ragon layya? Bayan sallah da sati daya idan ka na son sayen ragon suna a Abuja sai ka yi tafiya mai nisa. To mene ne abin a rika takura musu.”

Shi kuwa Malam Ibrahim, wani dillali, cewa ya yi. “duk wanda ka ga ya na dillancin raguna a wurin nan, wallahi talauci ne ya sa ya ke yi, ba neman kudi ba ne. Ba ni da jari ko na naira dubu daya. Ya kamata gwamnati ta fahimci cewa tunda ba haurawa gidan attajirai za mu yi mu saci tuwon sallah ba, a rika barin mu mu na hada-hadar nan. Ko ba komai mu ma a gidan mu, mu ci tuwon sallah, kuma mu dinka wa yaran mu kayan sallah.”

Share.

game da Author