Wani kwamandan Boko Haram da aka bada sunan sa Isma’il, ya ce shi ne ya jagoranci sace ‘yan matan Chibok sama da 200 da aka yi cikin 2014.
Isma’l wanda ya yi saranda ga sojojin Najeriya eriya, ya ce ya kuma jagoranci wasu hare-haren, amma ya na mai nadamar abin da ya aikata. Haka ya bayyana a cikin wata hira da PRNijeriya ta yi da shi.
Isma’il dai shi ne kuma ya jagoranci wani mummunan kisa da Boko Haram su ka yi a Madagali.
Auwal Isma’il dai ya na ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen tona inda Boko Haram su ke boye. Ya kuma sa wasu manyan Boko Haram sun yi saranda.
“Ni da Abu Hafsat ne mu ka jagoranci sace matan Chibok, Mu muka jagoranci kai hari a Bama, Gwoza, Limankara, Bita, Basso, Madagali, Chibok, Pulka, Firgi da Mubi.”
“Madagali nan ne garin mu. Amma da mu ka isa, ni da Adam Vitiri, Abu Adam da Habu Kudama, mu ka jagoranci kai harin 2014. Mu ka kashe dalibai a sakandaren Sabon Garin Madagali.”
“A daya daga cikin harin da mu ka kai, na sato mata ta mai suna Maryam, wadda a yanzu haka har mun haifi ‘ya’ya biyu da ita a Dajin Sambisa.”
“Ina mai nadamar yaudara ta da aka yi aka sa ni wannan mummunar hanyar kisan jama’a.
” A yakin Konduga, inda ni da wasu ne mu ka jagorance shi, na rasa kafa ta ta dama, amma duk da haka, Sheikh Shekau ya ce a ba ni keke mai taya uku na rika kai hari da shi. Haka na rika yi kafin na yi saranda.”
Ya ce ya yanke shawarar saranda saboda ya gaji da kisan bayin Allah haka nan.
Discussion about this post