Kusan rokon Audu Ogbe muka yi ya bimu a wannan tafiya– Osinbajo

1

Mukaddasgin Shugaban Kasa Yemi Osinbajoo ya ce gwamnatin Buhari kusan rokon Audu Ogbe tayi don ya zo a tafi dashi a wannan mulki.

Osinbajo Ya fadi Haka ne a wani taron wayar da kai da akayi a Abuja.

Ya ce bayan an lura cewa Audu Ogbe ya kware sosai a harkar ayyukan noma sannan ya yi shiru kamar bashi, “shine muka ga ba za mu barshi ya ci gaba da ayyukansa shi kadai ya zo yay a kara bada gudunmuwarsa a kasar.”

Ya kara da cewa Najeriya ta mai da hankalinta sosai kan harkar noma yanzu kuma ana sa ran da irin kwarewa ta ministan wato Audu Ogbe, kasar za ta kai ga ci.

Share.

game da Author