Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ki halartar taro da gwamnati

0

Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASSU, ta ki halartar taron daidaitawar da aka shirya za ta yi da gwamnatin tarayya.

Kungiyar ta ki halartar taron ne, wanda ake ganin za a zauna a samu maslahar kawo karshen yajin aikin da malaman ke yi.

Kin halartar taron dai ta ki halartar taron bisa dalilin da ta bayyana cewa ta rigaya ta aika wa gwamnatin tarayya da bukatun da ta ke so a biya mata, wanda ta ce har yanzu ta na kan bakan ta.

A cikin wata takarda da Shugaban Kungiyar, Biodun Ogunyemi ya saw a hannu, ya ce ba za su je zaman tattaunawar ba, domin sun aika da bukatu da sharuddan da sai an cika musu sannan za su janye yajin aikin wanda suka fara makwanni biyu da su ka gabata.

“Tun a ranar 17 Ga Augusta, 2017, mu ka yi taro da Ministan Kwadago da na Ilimi, su ka ce mu tuntubi mambobin mu sannan mu sake waiwayar su. Mun kuma tuntubi mambobin na mu, kuma mun aika wa gwamnati matsayin mu a jiya 28 Ga Satumba, 2017.”

Share.

game da Author