Kotu ta raba auren wata mata da tayi barazanar babbaka mijinta na aure

0

Wani magidanci mai suna Akibu Oyewole ya kai karan matarsa zuwa kotun karan dake Mapo a Ibadan jihar Oyo saboda barazanar banka masa wuta da ta yi da ‘ya’yansu.

Akibu ya fadawa kotun cewa ya auri mafadaciyar mace ce a matsayin mata.

Matar tasa ta taba gudu daga gidan aurenta inda ta kwashe masa kayansa kaf.

Ya ce ko da ta dawo gidansa bata bar halin tsiyarta ba domin wata rana ta kule shi a daki inda ta yi barazanar kona shi da wuta tare da yaran su sannan ta kashe kanta.

Saboda hakan ne Akibu ya roki kotu da ta warware auren dake tsakanin su domin ya gaji da zama da ita.

Omalara ta ce ba’a take yi masa a lokacin da ta ce za ta kona shi domin ta ba shi tsoro kawai. Ta kuma amince kotu ta warware auren su domin babu sauran kauna tsakaninsu.

Bayan sauraron su alkalin kotun Ademola Odunade ya warware auren kuma yaran za su zauna tare da mahaifiyar su sannan Akibu zai dinga biyan Omolara Naira 8,000 kowace wata domin kula da ya’yan.

Share.

game da Author