Kotu ta kwace gidan Dala Milyan 37.5 daga hannun Deizani

0

A yau ne Mai Shari’a Chuka Obiozor da ke Babbar Kotun tarayya ta Lagos ya kwace wani tangamemen gidan alfarma, mallakin tsohuwar ministar man fetur, Deizani Maduekwe.

Gidan dai ya na kan tsibirin Banana Island, wanda aka kiyasta kudin saya kai dalar Amurka milyan 37.5 Alkalin ya bayar da wannan odar karbe gidan bayan da Hukumar Hana Zambar Kudade, EFCC ta shigar da kara ta na neman a kwace gidan daga hannun ta.

Gidan dai ya na mai lamba 3, Block B, Bella Vista Plot, Banana Island a cikin Foreshore Estate. Katafaren gidan dai gida ne tangameme mai dauke da gidaje birjik har 24, da bangarori a cikin sa.

Kotu dai ta fara kwace gidan ne a ranar 19 Ga Yuli, 2017, inda alkali ya bada sati biyu ya ce mai gidan ta zo ta yi bayanin yadda gidan ya zama halak malak din ta a cikin sati biyu. Idan ba ta je ba kuma, to gwamnati za ta kwace shi, dungurugum daga hannun ta.

A yau Litinin an yi tsammanin zuwa Deizani, amma sai aka ji shiru, ko labarin ta babu. Nan take mai shari’a ya tabbatar da karbe gidan, ya fita daga hannun ta faufaufau.

DZ2

Share.

game da Author