Kasurgumin mai garkuwa da mutane, Evans, ya amsa laifin sa a kotu

0

Kasurgumin mai garkuwa da mutane, kuma biloniya, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da suna Evans, ya amsa laifukan da kotu ke tuhumar sa da aikatawa.

An sake gurfanar da shi ne yau Labara a babbar kotun Ikeja da ke Lagos, a gaban Mai Shari’a Abdul’aziz Anka, inda bay i doguwar ja-in-ja da shi ko da lauyoyin sa, sai ya amsa laifukan sa kawai.

Evans ya yi kaurin suna wajen sace hamsahakan masu kudi ya na yin garkuwa da su, ya na karbar makudan kudade. an ce duk ta nan ne ya kudance, har ya zama biloniya.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya dai ta shafe shekara shida ta na neman sa, sai cikin watanni biyu da suka gabata ne aka yi masa kofar-raggo, aka cafke shi.

Share.

game da Author