Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef ta ce bincike ya nuna cewa duk da cewa mata da dama a Najeriya na shayar da jariransu nono wadanda suke haka har ya kai tsawo watanni shida kashi 25 bisa 100 ne kawai.
Jami’in hukumar Stanley Nanama ya yi kira ga mata da su dauki shayar da ya’aynsu nono da mahimmanci. Sannan ya zayyano kadan daga cikin amfanin da nono yake yi wa jarirai.
1. Shayar da yaro ruwan nono da zaran an haife shi na hana yaro mutuwa.
2. Yana taimakawa yaroo ya girma yadda ya kamata.
3. Yana kare yaro daga kamuwa daga cututtuka kamar su kenda, tarin lala, sankarau da sauransu.
4. Shayar da yaro nono na taimaka wa iyayen wajen rage kashe kudin siyan abincin da zasu ci.
5. Shayar da yaro nono wata dabara ce na ba da tazarar haihuwa domin yana jinkirta daukar ciki.
6. Yana kare mata daga kamuwa da cutar dajin dake kama nono da mahaifa.
7. Nono na bunkasa kwakwalwan yaro.
8. Yana kuma kara musu karfin kashi.
9. Yana kare uwa daga kamuwa da cutar siga (diabetes).
10. Yana rage kiba a jikin uwa bayan ta haihu musamman wajen maida cikin yadda yake kafin ta haihu.