Gwamnatin Jhar Kaduna ta bayyana cewa ta kashe sama da naira biliyan 4 wajen maida makarantun gwamnatin jihar zuwa na zamani.
Kwamishinan Ilmin Kimiyya da Fasaha na jihar, Andrew Nok ne ya bayyana haka ranar Alhamis.
Ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke zantawa da wata kungiyar ‘yan social media a jihar. Ya kara da cewa kashi 35 bisa 100 na kasafin 2017 na jihar duk ya tafi ne wajen yi wa harkokin ilimi hidima, yayin da aka raba kujeru da tebura har dubu saba’in da takwas a kan kudi naira miliyan 710.
“Mun gano cewa sama da rabin yaran mu su na zaune ne a kan daben cikin ajujuwan su, sai mu ka hanzarta samar da tebura da kujeru a makarantun sakandare da firamare.”
Ya ce ma’aikatar sa ta kuma samar da kayayyaki, ta horas da malamai kuma ta bayar da tallafi karo ilmi.
“Mun gina makarantu a cikin shekaru biyu; kashin farko na aikinmu ya kunshi sabunta makarantu 15 a cikin jihar wadanda mu ke da nufin mayar da su na kwana, kamar yadda su ke a da can, kuma mu ka samar musu da dukkan ababen da ake bukata a makarantun kwana.”
Nok ya ce aikin da ake gudanarwa a wadannan makarantu ya kusa kammalauwa, domin an ci karfin ayyukan da kashi 80 bisa 100.
A ta bakin sa, an daina amfani da bakin allon rubutu wanda ake darza wa alli, saboda barazanar da ake samu ga lafiyar masu amfani da shi.
“Dalili kenan mu ka samar da allon rubutu na zamani har guda 1000 ga makarantu.” Inji kwamishinan.
Ya ce kuma sun kashe sama da naira miliyan shida wajen sayen littattafan karatu ga makarantun sakandaren jihar.