Jihar Kebbi za ta fara sayar da shinkafa kasashen waje

0

Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu, ya bayyana cewa jihar sa na nan na shirya yadda za ta fara fitar da shinkafa da dabbobi ta na sayarwa kasashen waje.

Bagudu ya yi wannan jawabi a ranar Alhamis lokacin da ya karbi bakuncin wasu kwararru kan karkokin noma, da su ka kai ziyara daga Cibiyar Inganta Dabarun Noma ta Kasa da Kasa da ke Ibadan.

Ya ce jihar Kebbi ta samu karin noma shinkafa da alkama har kusan nunki uku fiye da wanda ta ke nomawa a da. Ya kuma kara da cewa Jihar Yobe ce ta biyu wajen kiwon dabbobi a kasar nan.

Bagudu ya yi kira ga kungiyoyin da ke binciken dabarun noma na kasa da kasa da su yi tsatstsauran nazarin tsarin inganta dabarun noman jihar Kebbi, wanda gwamnatin sa ta shigo da shi. Ya na mai karawa da cewa hakan zai sa a maida hankali wajen kara habbaka albarkar da ke tattare da harkokin noma a jihar.

Ya ce har ila yau jihar Kebbi na da albarkar filaye na noman gyada, waken soya, ayaba, doya, gero, rake, dawa, rogo da kuma citta.

Da ya ke jawabi, shugaban tawagar, Kenton Dashiell, ya ce cibiyar su ta samu karbuwa a duniya saboda shaharar ta wajen gudanar da bincike kan harkokin noma da albarkatun da ke tattare da shi.

Ya ce tawagar ta su ta je Kebbi ne domin ta samu karin sarken binciken albarkatu da dabarun noma a jihar.

Shi ma da ya ke jawabi, Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa, Sahabi Augie, ya ce kungiyar su za ta bada hadin kai ga cibiyar domin a kara habbaka noman shinkafa a jihar Kebbi.

Share.

game da Author