Shugaban hukumar kula da karbar haraji na jihar Kaduna KDIRS Muktar Ahmed ya ce tsakanin watanin Janairu zuwa Yulin shekarar nan hukumar sa ta tara kudin harajin da ya kai Naira biliyan 9.6.
Ya ce mafi yawa daga cikin kudin da ga harajin da ake cirewa daga albashin ma’aikata ne.
Ya ce sauran wuraren da suka sami kudaden harajin ya hada da asibitoci da makarantun dake jihar.
Muktar Ahmed ya kara da cewa jihar Kaduna na da hanyoyin karban haraji da ya kai miliyan uku zuwa hudu amma abin da hukumar su take yi aiki da shi 400,000 ne kawai.
Saboda haka gwanatin Jihar na kokarin ganin ta kafa dokar da zai bata ikon karban haraji daga duk kafofin da ya kamata a karba a jihar wanda hakan zai taimaka wajen samar wa mutane ababen more rayuwa.
Muktar Ahmed y ace suna iya kokarin su wajen ganin sun kawar da matsalolin da hukumar ke fama da su wanda ya hada da rashin biyan haraji daga mutane da wawushe kudin harajin da wasu ma’aikatan ke yi.
Discussion about this post